Masana ilimin dubar wata a Najeriya sun ce ba za a haifi Jinjirin watan Shawwal ba a Najeriya sai kusan goma na daren Assabar.
Simwal Usman Jiblir mamba a kwamitin dubar wata wanda ya ke ƙarƙashin majalisar ƙoli ta addinin musulunci ne ya bayyana haka a cikin wata fira da BBC na ɗora a shafinta na Facebook ya yau Assabar.
Ya ce yau za a haifi jinjirin watan ne na shawwal da daddre a yau Assabar da ƙarfe 9 da minti 28 na dare.