Bayan Tantance Ƴan Takara PDP Ta Hana Mutum 2 Yin Takara A 2023

Rahotanni na nuna cewa babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta haramta ma wasu mutum biyu daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa 17 a kakar zaben 2023 yin takara ƙarƙashin jam’iyyar.

BBC Hausa ta ruwaito cewa Premium Times da ta ruwaito labarin ta ce shugaban kwamitin tantance ƴan takarar David Mark, bai kai ga bayyana sunayen mutum biyun da aka hana ma yin takarar ba da kuma dalilin rashin cancantarsu.

PDP dai ta aikin tantance yan takar ne a cikin satin jiya kuma daga cikin ƴan takarar da aka tantance a ranar Juma’a a hedikwatar jam’iyyar a Abuja sun hada da tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon shugaban Majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan Kwara Sanata Bukola Saraki da gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal da gwamnan Bauchi Bala Muhammad da Peter Obi da Pius Anyim.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram