Ƴan Sanda Sun Kama Ƙwaya Ta Kimanin Naira Miliyan 3 A Legas

Rundunar ƴan sanda a Jihar Legas ta kama ƙwaya, da a ke zargin tabar wiwi ce da kuɗin ta ya yi kimanin Naira Miliyan 3.

Kakakin Rundunar, SP Benjamin Hundeyin ne ya tabbatar da kama ƙwayar a wata sanarwar da ya fitar a yau Lahadi a Legas.

Ya ce jami’an rundunar sintirin gaggawa ne, a yayin sintirin su na yau da kullum, su ka kama motar da misalin ƙarfe 4 na safe a ranar 29 ga Afrilu a unguwar Surulere.

Ya ce kayan da ke kunshe a buhuhuna 10, an ɗauko su ne a motar haya ta Legas mai lambar LND 995 XT da ta taho daga Iddo zuwa inda za a sauke kayan a Mushin.

Amma sai jami’an sintirin gaggawa su ka tare motar.

Kakakin Rundunar ya ƙara da cews an kama direban motar, Amodu Agbaje, inda abokan tafiyar sa kuma su ka tsere.

Direban ya ce Naira dubu 25 a ka bashi domin ya kai kayan wani waje.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram