Wasu al’ummar Musulmi a jahohin Sokoto da Kebbi da ke Arewacin Najeriya sun gurdanar da Sallar Idin ƙaramar sallah a yau Lahadi.
BBC Hausa ta ce a jihar Sokoto, Sheikh Musa Lukwa ne ya jagoranci Idi da mabiyansa a ranar Lahadin.
Hakazalika a garin Jega na jihar Kebbi sun gudanar da Sallarsu da Idi.
Mai alfarma sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya ayyana ranar Litinin a matsayin ranar Sallah bayan kasa ganin watan Shawwal a ranar Asabar.
Samun irin wannan saɓani ba sabon babu ba ne a Najeriya.