Nura Khalil Zai Fito Takarar Gwamnan Katsina A Jam’iyyar NNPP

Fitaccen ɗan siyasar nan wato Injiniya Nura Khalil ya amince zai tsaya takarar gwamnan katsina a jam iyyar NNPP mai alamar kayan Marmari.

Wani jigo a jam iyyar ya tabbatar ma da jaridun katsina city news cewa sati mai zuwa injiniya zai yanki fom na tsayawa takarar kamar yadda jarifar ta faɗa.

Haka kuma jaridar ta ce ya yi kokarin magana da injinyan amma ba su samu dama ba saboda wayoyin shi basa tafiya.

Jaridar ta ƙara da cewa, in har Nura Khalil ɗin ya tsaya takarar wannan shine karo na huɗu da ya tsaya takarar gwamna inda ya yi biyu a jam iyyun Adawa ɗaya a jam iyyar PDP lokacin tana mulki sai kuma yanzu da zai fito a NNPP.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram