Mai martaba Sarkin Zazzau Ya Dakatar Da Hakimai 4

Mai martaba Sarkin Zazzau Malam Ahmad Nuhu Bamalli, ya dakatar da wasu hakimansa 4, jim kadan bayan sauka daga hawan Idi, sakamakon karya dokokin hawan Daba na masarautar.

Wannan na zuwa ne ta cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran masarautar, Abdullahi Aliyu Kwarbai, ya fitar, inda yace dakatarwar ta fara aiki ne nan take.

A cewar sanarwar hakiman da aka dakatar sun hadar Uban Garin Zazzau kuma hakimin Soba Alhaji Bashir Shehu Idris, da Sarkin Dajin Zazzau kuma hakimin Kubau Alhaji Shehu Umar Aliyu.

Sauran sun hadar da wakilin Birnin Zazzau Alhaji Suleiman Ibrahim Dabo da kuma Garkuwan kudun Zazzau Alhaji Muhammad Sani Uwais.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram