Gwamna Badaru, Akpabio Sun Bayyana Aniyarsu Ta Gaje Kujerar Shugaban Ƙasa Buhari

Gwamnan jihar Jigawa, Muhammad Badaru Abubakar, da ministan harkokin Neja Delta, Sanata Godswill Akpabio, sun bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC.

Gwamnan ya samu damar siyan from din nagani inaso a hedikwatar jam’iyyar ta kasa da ke Abuja ranar Laraba.

Tun da farko dai an alakanta Badaru da takarar sanata kafin zaben 2023, amma rahotanni sun ce ya sauya shawararsa biyo bayan taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC mai mulki a gidan gwamnati a daren ranar Talata.

Ko da yake ba a san dalilin da ya sa ya sauya ra’ayin ba, an ce gwamnan ya shaida wa mahalarta taron cewa abokanan aikinsa ne suka matsa masa lamba don ya tsaya takarar shugaban kasa.

Mai baiwa gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai Habibu Nuhu Kila, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya ce “gaskiya gwamna Badaru ya tafi Abuja ne domin karbar fom din tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023.”

Ya ce yana da kwarewa a fannin shugabanci, inda ya kara da cewa idan aka ba shi dama ya gaji Buhari, zai ci gaba da “tabbatar da manufofin shugaban kasa.”

A halin da ake ciki, Akpabio ya kuma yi alkawarin ba zai bari Najeriya ta lalace ba, yana mai cewa zai kawo gyara, mutunci, mutuntawa da kuma taimakon ‘yan Najeriya.

Da yake magana a ranar Laraba ga dimbin jama’a a lokacin da ya ke bayyana kudurinsa a filin wasa na Garin Ikot Ekpene, tsohon Gwamnan Jihar Akwa Ibom ya bayyana cewa zai kawo cigaba a kasar nan kamar yadda ya kawo a Akwa Ibom.

Akpabio ya ce a matsayinsa na ministan harkokin Neja Delta, ayyukan tituna 88 da an yi watsi da su, amma saboda tsoron binciken kwakwaf da hukumar ta fara, ‘yan kwangilan sun kammala su.

Ya ce duk da irin kwarewar da yake da shi a matsayinsa na gwamna da minista ne ya ba shi damar ganin cewa zai iya zama shugaban kasa.

“Kun ji sanarwa da yawa amma wannan ba sabon abu bane. Ba wai kawai saƙon bege ba ne, ci gaba mai kyau, kuma saƙo ne na maido da martabar ku, mutunta ku a yankin ECOWAS da sauran ƙasashen waje.

“Ina neman takarar don na zama shugaban ku a zaben shekarar 2023. Ina gode wa shugaban kasa bisa damar da aka bani na samun ci gaba fiye da Wanda na samu a jihar Akwa Ibom. Shugaban kasa yana yaki da cin hanci da rashawa yadda ya kamata.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram