Gwmanan Jahar Anambra Farfesa Chukwuma Soludo a ranar Laraba ya ayyana Dokar ta ɓaci akan matsalar tsaro da ɓangaren gine-gine a Jahar.
Soludo ya baiwa Al’ummar sa tabbacin cewa zai mayar da Jahar wurin shaƙatawa.
Gwamnan ya bayyana haka a Awka a ranar Laraba a lokacin taron gari duka da masu riƙe da Sarautun gargajiya, Shuwagabannin Matasa, da sauran masu ruwa da tsaki a Jahar.
Yace an shirya taron ne domin baiwa Gwamnatin Jahar damar tattaunawa tare da ganawa da masu ruwa da tsaki da dama domin cigaban Jahar.
Ya bayyana rashin jindaɗi na yawaitar matsalar tsaro a jihar, sai ya buƙaci Al’umma dasu bada rahoton duk wanda aka gani ba’a yarda dashi ba, yana mai cewa mutanen dake haifar da matsalolin suna tare da Jama’a.
Ya kuma bada tabbacin kammala dukkanin ayyukan da ya gada duk da ƙarancin kuɗaɗe.
Yace ” a yau na cika kwanaki 49 a ofis. Wannan shine karo na biyu da muka kira Wannan taron domin sanar daku irin ƙudirin mu na kawo cigaba a Jahar. Zamu sake kiran ku idan muka cika kwanaki 100 a ofis.