Yara uku, maza biyar da mace daya sun samu raunuka a lokacin da wata motar bas ta yi hatsari a Gwagwalada, babban birnin tarayya Abuja, kan hanyar Abuja zuwa Lokoja.
Wani ganau ya ce hadarin da ya faru da misalin karfe 3 na rana ya rutsa da wata motar bas Sharon mai lamba BWR 217 CG.
Ya ce motar bas din da ta taho daga mashigar Lokoja tana cikin tsananin saurin gudu a kusa da wata kan wata gada, ta rasa yadda za ta yi, sannan ta fada cikin magudanar ruwa.
Da aka tuntubi Kwamandan Sashen Gwagwalada na FRSC, ACC Olasupo Esuruoso, ya ce, “Har yanzu ina jira don samun cikakken bayanin hadarin daga wajen jami’an da suka je wurin domin ceto wadanda abin ya shafa zuwa asibiti. Zan dawo wurinku idan sun dawo.”
Hakazalika, wasu mutane biyu sun jikkata a wani hatsarin da ya faru a Kuchingoro dake kan titin filin jirgin sama a Abuja.
City & Crime ta tattaro cewa hatsarin ya rutsa da wata mota kirar Toyota mai lamba BKW 140 XA da wata motar bas mai lamba BL 842 RBC.
Wani jami’in hukumar FRSC da ya so a sakaya sunansa ya tabbatar da faruwar hatsarin, ya kuma kara da cewa an kai wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Garki.