Buhari Ya Yabawa David Umahi Daya Canja Sheƙa Zuwa APC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana kudirin gwamnatin tarayya na karbar ragamar tafiyar da jami’ar King David ta kimiyya da fasahar likitanci ta jihar Ebonyi.

Makarantar dake a unguwar Uburu, mahaifar gwamnan jihar, David Umahi.

Majiyar Jaridar Jakadiya ta ruwaito, Buhari ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi ga masu ruwa da tsaki da kuma shugabannin siyasa a ziyarar kwanaki biyu da ya kai jihar.

Shugaban wanda ya yabawa gwamnan bisa sauya sheka da ya yi a kwanakin baya daga babbar jam’iyyar adawa ta PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki, ya ce wannan shawara ce mai kyau.

Shugaba Buhari ya ce, “Na je jihar Ebonyi ne a shekarar 2017 a kashi na biyu na gwamnatina ta farko, domin kaddamar da harsashin ginin kantin sayar da kayayyaki da sauran ayyuka, kuma an yi mini tarba mai kyau.

“Gwamnatin jihar Ebonyi karkashin jagorancin David Umahi ba ta yi kuskure ba wajen sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC. Kuma ina yaba masa (Umahi) da ya shigo jam’iyyar a tsakiya domin ciyar da Jihar gaba.

“Na yanke shawarar karbe Jami’ar Kimiyya da Fasahar likitanci David da ke unguwar Uburu domin zama cibiyar tarayya. Za a fara aikin karbar ragamar mulki nan ba da jimawa ba.”

A martanin da ya mayar, Umahi ya nuna jin dadinsa ga Buhari da ya zo Ebonyi, musamman a shekarar 2017 lokacin yana jam’iyyar adawa ta PDP.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram