Da Ɗumi-Ɗuminsa: Tsagin Ganduje Ya Doke Na Shekarau A Kotun Ƙoli

Kotun Ƙoli ta kori ƙarar da ɓangaren tsohon gwamnan Kano na APC, Ibrahim Shekarau ya shigar yana ƙalubalantar hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi na cewa zaɓen shugabannin jam’iyar da tsagin Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi ba sahihi ba ne.

Kotun Ƙolin, a yau Juma’a, ta tabbatar da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta yanke, wanda ta tabbatar da sahihancin zaben shugabanni da bangaren Ganduje ya yi, inda Abdullahi Abbas ya zama shugaban jam’iyar APC na Jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram