Yanzu-Yanzu: Emefiele Ya Shiga Cikin Masu Takarar Shugaban Ƙasa, Ya Sayi Fom ɗin Miliyan 100

Yanzu-Yanzu: Emefiele ya shiga cikin masu Takarar Shugaban Ƙasa, ya sayi Fom ɗin Miliyan 100

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya sayi fom din nuna sha’awar neman tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Emefiele ya karbi fom din Naira miliyan 100 daga hannun sakataren jam’iyyar a International Conference Centre (ICC) da ke Abuja, a safiyar Juma’a.

Hakan dai ya sanya ake ta cece-kuce akan sha’awarsa ta neman ya gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A watan Fabrairun shekarar 2014, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nada Emefiele, sa’o’i kadan bayan ya sanar da dakatar da tsohon gwamnan bankin na CBN wato Sanusi Lamido.

A shekarar 2019, tsohon Manajan Daraktan Bankin Zenith ya kafa tarihi a matsayin Gwamnan CBN na farko da aka sake nada shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram