Hukumar Zaɓe ta Ƙasa Mai Zaman Kanta, IMEC ta gargaɗi jam’iyyu da su yi biyayya ga wa’adin da ta sanya na yin zaɓukan fidda-gwani na tunkarar zaɓukan 2023.
Kwamishina, kuma Shugaban Jwamitin Bayanai da Wayar da kan Masu Zaɓe na INEC, Festus Okoye ne ya yi gargadin a jiya Alhamis a wata sanarwar da ya fitar.
Okoye ya yi tuni cewa tun a 26 ga watan Fabrairu, 2022 INEC ta fitar da jadawalin zaɓukan 2023, inda ta kuma sanya 4 ga watan Afrilu zuwa 3 ga watan Yuni a matsayin lokacin da jam’iyun za su yi zaɓukan fidda-gwani.
A cewar sa, duk wani zaɓen fidda-gwani da a ka yi shi a bayan wa’adin da Hukumar ta sanya to ba karɓaɓɓe ba ne.
Ya ƙara da cewa dukka jam’iyyu 18 ɗin an kai musu sanarwa da jadawalin yin manyan tarukan su, zaɓen shugabanni da kuma zaɓen fidda-gwani kamar yadda sashe na 82(1) na dokar zaɓe ta 2022 ya tanada.
Ya tabbatar da cewa wa’adin yin zaɓukan na nan a ranar 3 ga watan Yuni babu wani canji, inda hukumar ta hori ƴan jam’iyyun da su tabbatar sun yi zaɓukan fidda-gwani lafiya ba tare da rigima ba.