Dan Wasan Dambe Mike Tyson Zai Bada Kyautar Dalar Amurka Milyan 10 Ga Duk Wanda Zai Yarda Ya Auri Diyarsa

Shararren dan wasan damben nan dan kasar Amurka, Michael Gerard Tyson ya shelanta kyautar zunzurutun kudi talar Amurka milyan 10 ga duk mutumin da ya yarda ya auri diyarsa.

DCL Hausa ta ruwaito cewa diyar ta sa mai suna Mitchell Tyson tana da kimanin shekaru 32 a duniya.

Tyson da aka fi sani da suna Iron Mike da kuma Kid Dynamite a lokacin da yana farko-farkon tashensa a fagen wasan dambe daga bisani kuma aka rinka kiranshi da sunan “The Baddest Man on the Planet.

Hakazalika dan wasan ya yi dogon zango a fagen wasan damben inda ya kashe tsawon shekaru 20 yana kan ganiyarsa tun daga shekara ta 1985 har zuwa 2005.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram