Mai taimaka wa shugaban kasa Muhammadu Buhari kan sabbin kafafen yada labarai, Bashir Ahmad, ya mayar da martani kan rahotannin da ke cewa Darakta Janar na kungiyar yakin neman zaben Bola Tinubu, Abdulmumin Jibrin zai fice daga jam’iyyar APC ba.
Ahmad ya bayyana kwarin gwiwar cewa Jibrin ba zai bar jam’iyyar APC zuwa wata jam’iyyar siyasa ba.
Majiyar Jaridar Jakadiya ta rawaito cewa tsohon dan majalisar wakilai mai wakiltar kananan hukumomin Kiru da Bebeji ya ce zai fice daga APC.
Kofa ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook a ranar Asabar din data gabata.
Tsohon dan majalisar ya ce nan da sa’o’i 24 masu zuwa zai bayyana sabuwar jam’iyyarsa.
A cewar sa “Na baiwa APC duk gudunmawar da zan iya, don haka lokaci ya yi da zan ci gaba. Zan sanar da sabuwar jam’iyyata nan da sa’o’i 24 masu zuwa.
“Zan yi sanarwa a kan lokaci,” in ji shi.
Akwai rade-radin cewa Jibrin ya yanke shawarar ficewa daga jam’iyyar APC ne sakamakon rashin fahimta da aka samu tsakaninsa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a jihar Kano ciki har da Gwamna Abdullahi Ganduje.
Da yake mayar da martani, Ahmad ya ce APC za ta hada shi tare da magance duk wasu matsalolin da suka sa shi rashin kwanciyar hankali.
Ahmad ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa: “Ina da yakinin cewa Honorabul Abdulmumin Jibrin Kofa ba zai bar mu ba, jam’iyyar APC reshen jihar Kano za ta hada shi da shi, ta kuma nemo hanyar da za ta magance matsalar da yake da ita da jam’iyyar a matakin kasa Mu dangi ne.” a cewar Ahmad.