Rashin Hankali Ne A Riƙa Kira Ga Mahmood Ya Fito Takarar Shugaban Ƙasa – INEC

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa a ranar Lahadi a Abuja tayi Allah wadai da kiraye-kirayen da ake yiwa Shugaban ta Farfesa Mahmood Yakubu ya shiga a nemi Kujerar Shugaban Ƙasa a Shekarar 2023.

Babban Sakataren Ƴan Jaridu na Shugaban INEC Mr Rotimi Oyekanmi yana mai bayyana kiraye-kirayen a matsayin rashin aikin yi, kuma bazai faru ba.

“Hankalin mu yakai ga wani rahoton rashin sanin ya kamata cewa, kada ƴan Najeriya suyi mamaki idan Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ya nemi Takarar Shugaban Ƙasa.

“Abun rashin sanin ya kamata ne. Kuma bazai faru ba. Shugaban Hukumar a shirye yake domin gudanar da Sahihin Zaɓe mai Adalci.

“Nauye-nauyen sa a matsayin Shugaban Hukumar Zaɓe na Ƙasa, kuma mai tattara sakamako da sanar da wanda yaci zaɓen Shugaban, abun saɓa doka ne ya nemi Kujerar.

Ya ƙara dacewa, Farfesa Yakubu zai cigaba da gudanar da aikace-aikacen sa ba tare da tsoro ba, ko kuma goyon bayan wata Jam’iyya, ko Ɗan Takara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram