Abdulmalik Tanko ya Amsa Laifin Garkuwa Da Hanifa, Amma Ya Musanta Kasheta

Abdulmalik Tanko, mamallakin makarantar Hanifa Abubakar, mai shekaru biyar, ya sake musanta labarin yadda yarinyar ta mutu.

Ya musantawa ne a yayin zaman babbar kotu mai lamba 5, da ke zaune a Audu Bako, a yau Litinin.

Mai shari’a Usman Na’abba ne ya jagoranci zaman kotun na yau.

Tanko, wanda a baya ya amince da hada baki, ya musanta sauran tuhume-tuhume uku da ake tuhumarsa da su da suka hada da yin garkuwa da yarinyar da kuma kashe ta daga baya.

Yayin da yake mamsa cewa, ya Hanifa zuwa makarantarsa kuma ​​ya kulle ta, ya ce, “Ban tabbata ko ni ne mutum na karshe da na ganta a raye ba saboda tun da farko na sanar da wani game da lamarin. Ban kashe ta da guba ba. Na bar ta tana barci na dawo na ga ta mutu.

“Ni kaina, wanda ake tuhuma na biyu da na uku ba su san yadda ta mutu ba.”

Idan ba’a manta ba, Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewa an sace Hanifa ne a ranar 4 ga Disamban shekarar 2021, a kan hanyarta ta komawa gida daga makarantar Islamiyya, kuma daga baya aka gano cewa an kashe ta.

Tun da farko Tanko ya amsa laifin yin garkuwa Hanifa, da wanda ya ce, ya kashe ta ne da gubar bera na Naira 100 kafin ya binne ta a wani kabari mara zurfi a daya daga cikin makarantunsa.

An gurfanar da mutanen uku Abdulmalik tare da abokinsa, Hashim Isyaku da Fatima Bashir a gaban wata babbar kotun jihar Kano bisa laifuka biyar da suka hada da hada baki, garkuwa da mutane, daurewa, da kuma kisan kai wanda ya sabawa sashi na 97, 274, 277, 221 na kundun dokar penal code.

Sai dai daga bisani Mai shari’a Usman Na’abba ya dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Mayu shekara Nan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram