Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da cafke wasu mutane 128 da take zargin ‘yan daba ne a yayin gudanar da bukukuwan Sallah Eid-El-Fitr a fadin masarautun jihar biyar.
Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Haruna Kiyawa ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a garin Kano.
Ya ce kamen ya yi daidai da umarnin babban sufeton ‘yan sandan kasar na samar da isasshen tsaro a lokacin bukukuwan Sallah.
A cewarsa, an kama mutane 128 da ake zargin ’yan daba ne a lokacin bikin “ sallar Eid karama” da “Hawan Daushe” da “Hawan Nassarawa” da “Hawan Fanisau” a dukkanin masarautun jihar biyar dake fadin jihar.
Ya ce an kama wadanda ake zargin ne da muggan makamai, da kwayoyi masu sa maye, da kuma zargin laifukan sace-sace.
Kiyawa ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar ya godewa gwamnati da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki bisa hadin kai da goyon bayan da suke bai wa rundunar.
Kiyawa ya ce za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala gudanar da bincike.