Idan Naci Zaɓe, Zan Ƙara Yawan Jami’an Tsaro A Najeriya — Inji Atiku

Atiku Abubakar ya ci alwashin ɗaukar sabbin jami’an tsaro maza da mata aiki domin magance matsalar tsaro idan ya ci zaɓen 2023.

Atiku, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyar PDP ya faɗi haka ne a Akure a yayin gana wa da wakilai masu zaɓe da kuma shugabannin jam’iyar a jiya Lahadi.

Da yanke jawabi, Atiku ya kuma yi alƙawarin samar da kayayyakin aiki masu yawa ga ƴan sanda, inda ya ce samar da kayan aiki itace hanya mafi inganci wajen magance matsalar tsaro a ƙasa.

Ya kuma gode wa mutanen Jihar Ondo bisa amince wa da shi da kuma zaɓar sa a matsayin ɗan takara a zaɓen 2019.

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasan ya kuma yi kira ga wakilan zaɓen da su sake zabar sa a zaben fidda-gwani da za a fafata a ranar 28 ga watan Mayu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram