Wani Masanin Tattalin Arziki Yace Auren Mace Fiye Da Ɗaya Yana Haifar Da Talauci

Dakta Chiwuike Uba, wani masanin tattalin arziki ya dora alhakin yawaitar talaucin da ake samu da Auren wuri da kuma na mace fiye da daya.

Uba, wani mai bincike dake aiki da cibiyar African Heritage ya bayyana hakan ne a Enugu ranar 5 ga watan mayun da muke ciki yayin da yake gabatar da sakamakon bincikensa kan “Yadda Auren mace fiye da daya ke haifar da Talauci a fadin Najeriya”.

Masanin ya bayyana cewa auren wuri na da alaka da yawaitar samun ‘ya’ya masu tarin yawa wanda yake tasiri ga Talauci da tsaro.

Acewarsa mai mako jinkiri wajen yin aure har zuwa shekaru 20 zuwa 30, mata na yin aure tare da haifar ‘ya’ya tun suna da kananun shekaru.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram