Yanzu-yanzu: Saraki Zai Gana Da Obasanjo Kan Batun Neman Takarar Sa Ta Shugaban Kasa

 

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Dakta Bukola Saraki, ya kai ziyara gidan tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, jihar Ogun, a wani bangare na tuntubar juna kan batun neman takararsa ta shugabancin kasa.

Saraki ya isa gidan Obasanjo dake cikin dakin karatu na Olusegun Obasanjo Presidential Library (OOPL), Abeokuta, da misalin karfe 12:04 na rana.

Ya isa ne tare da tawagarsa ciki har da tsohon shugaban jam’iyyar PDP na kasa, Kawu Baraje, da dai sauransu.

Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a halin yanzu Saraki yana jiran Obasanjo yana wata ganawar sirri da wasu dattawan Igbo a dakin taro na OOPL.

Wakilinmu ya tattaro cewa Saraki ya je jihar ne domin yin jawabi ga wakilan jam’iyyar PDP gabanin gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa na jam’iyyar.

Tsohon gwamnan jihar Kwara bayan ganawarsa da Obasanjo, ana sa ran zai gana da wakilan jam’iyyar PDP a sakatariyar jam’iyyar da ke Abeokuta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram