An Ceto Mutane 15 Da Aka Yi Garkuwa Da Su Tare Da Mashina A Niger

Tawagar Ƙwararrun Ƴan Sanda da Ƴan Bigilanti sun ceto aƙalla Mutane 15 daga hannun Ƴan bindiga a ƙauyen Jellako na Ƙaramar Hukumar Rafi ta Jahar Niger.

Rundunar Ƴan Sandan Jahar wadda ta bayyana haka ta hannu Mai Magana da Yawun Rundunar DSP Wasiu Abiodun a Minna, yace haɗakar Jami’an tsaro sun yi bata kashi tsakanin su da ƴan bindigar wanda ya yi sanadiyyar ceto mutane 15 daga inda aka ɓoye su.

Ya bayyana cewa, a dalilin ƙarfin ruwan wuta da ƙwararrun Jami’an suka yi, ƴan bindigar sun riga daga wurin, a yayinda wasu suka tsere cikin daji da harbin bindiga, duk da an samo Babura guda biyu.

A cewar sa “akwai samame da muke cigaba da kaiwa na magance ƴan bindiga da sauran ƴan ta’adda a Jahar, a ranar 9 ga watan 5 na Shekarar 2022 da misalin ƙarfe 8 da 30 na dare, sakamakon bayanan sirri da aka samu cewa an ga ƴan bindiga kusa da ƙauyen Jellako na Ƙaramar Hukumar Rafi, haɗakar Jami’an tsaron da ƴan Bigilanti sun saurin zuwa wurin inda suka yi faɗa da ƴan bindigar”.

Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan yace an samu nasarar ceto su ba tare da ko rauni ba, kuma an kaisu wani Asibiti domin duba lafiyar su.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram