Sarkin Yaƙi a Ƙasar Yarbawa Wato- Aare Ona Kakanfo, Iba Gani Adams yace yajin aikin Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Najeriya ASUU abun damuwa ne.
Basaraken gargajiya ya shaidawa Gwamnatin Tarayya cewa an tauye makomar Matasan Najeriya.
Adams yayi jawabi a Lagos a Jiya a lokacin bikin ranar haihuwar sa karo na 52.
Ya bayyana damuwa na kasawar Gwamnati wajen kawo ƙarshen matsalar yajin aikin na tsawon shekaru.
“Ɗaliban Najeriya bazasu iya jure ƙara share satittika 12 a gida”, Gargaɗin shi.
Adams yayi kira ga Hukumomin da abun ya shafa dasu magance matsalar dake akwai a ɓangaren Ilmi.
“Ina jin takaici na yadda nake ganin Ɗaliban Najeriya suna zaune a gida. Wannan yana taɓa tunanin su, kuma yana haifar da matsala a ƙasa” .