Da-Dumi-Dumi: Bom Ya Tashi Kusa Da Wani Sansanin Sojin Jalingo

Wani Abu da Ake kyautata zaton bom ne ya sake fashewa a garin Jalingo na jihar Taraba.

Fashewar wadda ta afku a daren jiya Talata da misalin karfe 9 na dare ta faru ne mitoci kadan da sansanin sojin garin jalingo

Wani ganau da ya zanta da manema labarai ya ce, Wani Mutum ne dayazo wucewa ya jefa abun fashewar ga sansanin sojin.

Wannan dai na zuwa ne wata guda da faruwar Makamancinsa a yankin Iware dake garin Ardo-Kola da yayi sanadiyar asarar rayuka da dukiyoyin masu yawa.

Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai, Kakakin rundunar Yan sandan jihar Taraba Usman Abdullahi ya ce, tabbas ya Ji karar fashewar Amma Bai da tabbaci ko akwai Wanda ya Mutu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram