Har Faɗa An Yi Da Wuƙaƙe A PDP Ta Katsina Saboda Neman Shugabanci – Muttaqha Rabe

Shugaban cibiyar PLBC kuma tsohon shugaban asusun rarar man fetur na Najeriya, Muttaqha Rabe Darma ya bayyana dalilanshi da suka sanya shi ya fice daga jam’iyyar PDP a Katsina.

Muttaqha Rabe wanda ya ce akwai kusan dalilai 10 da ya zayyana a cikin takardar da ya rubuta ma shugaban jam’iyyar na mazaɓarshi.

A yayin da jakadiya ke zantawa da shi dangane da fitar tasa daga jam’iyyar ya ce har faɗa an yi da wuƙaƙe a jam’iyyar saboda neman shugabanci da kuma badaƙalar handame kuɗaɗen sayen fam fam da kuma yin shugabanci ta hanyar bautar da mutane, ya ce wannan na daga cikin dalilan na shi.

Darma wanda ya kira jam’iyyar da zama kamar wata ƙungiyar asiri ya ce in mutum ba ya cikin da’irar mutanen da ake so ko in mutum ba ya bauta ma su shugabannin to duk iyawarshi ba za a tafi da shi ba.

Muttaqha Darma ya ce shi ba wai ba ya da ubangida ba ne yana da kuma shi ne marigayi Malam Umaru Musa Ƴar’adua sannan ya yarda da shugabanci amma kuma shi ba bagidaje ba ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram