Jahar Kwara Ta Samu Kujeru 1,406 Domin Aikin Hajjin Bana

Shugaban Hukumar Alhazai ta Jahar Kwara Alhaji AbdulGaniyu Ahmed yace kimanin Mahajjata 1,406 daga Jahar zasu gudanar da Hajjin wannan Shekarar a Ƙasar Makka.

AbdulGaniyu a lokacin da yake jawabi ga Manema labaru a Ilori a ranar Talata yace an zaɓi maniyyata aikin Hajji 1,600 wanda suka biya kuɗi domin gudanar da Hajjin wannan Shekarar a Jahar a Shekarar 2020, amma basu je ba, sakamakon ɓarkewar Annobar Covid-19 data afku a faɗin Duniya.

Ya kuma baiwa Musulmi tabbacin ƙudirin Hukumar na yin shirye-shirye domin Hajjin Shekarar 2022.

“Mutane 1,600 suka biya aikin Hajji a Shekarar 2022 amma basu samu halin zuwa ba, sakamakon cutar Covid-19. Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Najeriya ta baiwa Jahar Kwara Kujeru 1,406 na wannan Shekarar”, Inji shi.

AbdulGaniyu ya ƙara dacewa sakamakon ƙarin kuɗin kujerar, yanzu ta tashi daga Naira Miliyan 1.5 zuwa Miliyan 2.3.

Yayi kira ga Al’umma wanda suka biya kuɗin Takarar da farko dasu ida cika kuɗin.

Ya jaddada cewa an kulle adireshin biyan kuɗin a ranar 7 ga watan Mayu, kuma duk wanda basu biya ba, to dole su jira sai shekara mai zuwa.

Ya bayyana cewa Hukumar bata da wani gurbi na wasu sabbin Mahajjata sakamakon waɗanda suka riga suka biya tunda farko.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram