An Kama Kansila Da AK-47 Kusa Da Maɓoyar Ƴan Bindiga A Kaduna

An cafke Kansila da AK-47 kusa da Maɓoyar Ƴan bindiga a Kaduna

Abdul Adamu Kinkiba Kansila a Karamar Hukumar Soba ta Jahar Kaduna an kama shi na bindiga AK-47 a kusa da Ƙaramar Hukumar Giwa ta Jahar.

Jaridar Daily Trust ta bada rahoton cewa, yankin yana kusa da Maɓoyar Masu Garkuwa Da Mutane na ƴan bindigar dake addabar mutane a sassa da dama na Jahar.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Soba Engineer Suleiman Yahaya Richifa ya tabbatar da kama Kansilan.

Ya bayyana cewa wanda ake zargin shine Kansila dake Wakiltar yankin Kinkiba ta Ƙaramar Hukumar.

Ya kuma ƙi cigaba da magana, yana mai ƙara dacewa “ina matuƙar mamaki akan labarin nan. Ku ƙyale Ni in Kammala jimamin haka.”

A lokacin da Majiyar Jaridar Jakadiya ta tuntuɓi Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar ASP Mohammed yace zai sake kira.

Yace “ina kan hanyata ta zuwa Masallaci yanzu, zan kira ka daga baya kaɗan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram