Tsohon Sakataren Gwamnatin jahar Katsina kuma mai neman jam’iyyar APC ta tsaida shi a matsayin ɗan takarar kujerar Gwamnan jahar, Mustapha Muhammed Inuwa ya ce ya zama wajibi ya fito ya nemi kujerar gwamnan Katsina.
Tsohon Sakataren ya bayyana haka ne a yayin wata fira ta musamman da gidan rediyon Alfijir ya yi da shi a ranar Larabar nan da ta gabata.
A cikin shirin an yi ma Mustapha Inuwa tambaya ko me ya sanya ya ke son ya zama gwamnan katsina? sai ya amsa da cewa ya fito takaran gwamna ne saboda al’umma, ya ce yana son ba kawo gudunmuwarshi ga jahar Katsin da kuma kawo sauye sauye da dama a cikin tafiyar siyaya.
Inuwa ya ce ai shi tunda dai har yana da kwarewa da kuma sanin makamar siyasa da hanyar da za a bi don ci gaban jahar ta katsina da al’ummarta to lallai in bai fito ba sai Allah ya tambaye shi.
Ya ce ba wai ya ce dole sai ya zama gwamna ba illa iyaka dai yana roƙon Allah in shi alheri ne to Allah ya ba shi in kuma ba alheri ba ne to Allah ya ba wanda ya ke shine al’heri ga jahar, ya ƙara da cewa shi jahar ce a gabanshi ba komai ba.