Naira Ta Sake Faɗi Ƙasa Warwas, Yanzu Ana Canjin Dala 1 Akan Naira 420

Naira ta sake Faɗi Ƙasa Warwas, yanzu ana canjin Dala 1 akan Naira 420

Kuɗin Naira a ranar Alhamis, ta faɗi Ƙasa warwas a hannun ƴan Kasuwa da hannun ƴan canji, inda ake canja ta akan Naira 420 a dukkanin Dala guda, ya faɗi kenan da kashi 0.30, tayi ƙasa fiye da yadda ake saida ta akan Naira 418.75 a ranar Laraba.

Ana ranar Alhamis an canje ta akan Naira 416.50 akan duk Dala guda.

Naira dai yanzu ana canjar ta akan Naira 444.00 akan duk Dala guda, wanda shine faɗin da Naira ta taɓa yi kafin taje Naira 420.

A kasuwancin da akayi da’ita a yau an saida ta akan Naira 412.38 akan Dala guda.

Kimanin Dala Miliyan 160 aka yi canjin ta a hannun masu canji na Gwamnati, da ƴan Ƙasa a ranar Alhamis.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram