Shuwagabannin Ƙungiyar Ƴan IPOB ta jaddada ƙudirin ta cewa ba zata kai hari ga Ƴan Arewa ko wanda ba Ɗan Biafra a yankin Inyamurai.
A cewar Ƙungiyar, Inyamurai mutane ne masu maraba da kowa da Kara, tana mai ƙara dacewa zata yi dukkanin abinda zata iya domin kula da wanda ba Ɗan Ƙasa ba a lokacin kai hari ko wani Lamari ba.
Ƙungiyar, wadda tace tana da Jami’an Sirri da suka gano cewa wani Labarin ƙanzon kurege dake fitowa daga Rundunar sojin Najeriya da sauran Hukumomin tsaro suna yin wani yunƙuri na shafe su daga yankin Kudu Maso Gabas, tare nuna yatsa ga IPOB.
Daraktan Yaɗa Labaru na IPOB Mr Emma Powerful ya bayyana haka a cikin wata sanarwa daya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar tace “akan wata sanarwa ta cikin Gida da Rundunar Soji ta fitar da IPOB ta samu ƙarƙashin jagorancin Mazi Nnamdi Kanu, muna Son jaddada cewa bazamu taɓa dukkannin wasu wanda ba ƴan Biafra ba da sauran Al’umma, kuma basu da shirin yakar ƴan Arewa dake zaune a yankin.