Ƴan bindiga Sun Yi Awon Gaba Da Ɗan Jarida A Zamfara

Wani Ɗan Jarida mai aiki da Gidan Rediyo da Talabijin a Gusau Kwamared Idris Haruna Magami ya shiga hannun masu garkuwa da mutane.

A cewar shaidar Gani da Ido, An sace Magami akan hanyar Gusau Ɗansadau a lokacin da yake kan hanyar sa ta zuwa garin su Magami, kilomita 40 daga Gusau, Babban Birnin Jahar bayan ya tashi daga aiki.

Kwamared Magami ya kasance sanannen Ɗan Jarida ne a Gidan Rediyo da Talabijin na Zamfara, musamman a shirin shi dayake gudanarwa na Hausa mai suna “Su duniya manya”.

A cewar Ɗan Asalin garin Magami Malam Almu “Idris Haruna Magami yana kan hanyar sa ta zuwa garin su tare da abokin sa, Alhaji Kabiru a lokacin da aka kaiwa Abun Hawan su hari.”

Almu ya bayyana cewar Alhaji Kabiru ya samu nasarar tserewa , a yayinda ƴan bindiga suka sace Idris Magami tare da tafiya dashi inda ba’a ida sani ba.

A cewar sa, tuni ƴan bindigar sun yi magana da iyalan Idris Haruna, amma har yanzu basu faɗi ko nawa suke buƙatar a biya su a matsayin kuɗin fansa.

Haka zalika, dukkanin wani yunƙuri na yin magana da Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Zamfara SP Mohammed Shehu bai samu ba a yayinda ba’a samu layin shi ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram