2023 Hamza Jibia Ya Roƙi Alfarmar A Zaɓi Majigiri

Hon. Hamza Yunusa Jibia ya gana da Shuwagabanni da Jagororin Jam’iyyar PDP na KaramarHukumar Jibia, ya roki Alfarmar su Zabi Majigiri

Shugaban Matasa mai barin gado na Shiyyar Arewa maso yamma (North West Zone), ya gana da Shuwagabannin Jam’iyyar PDP na karamar Hukumar Jibia a yau (12-05-2022), yayi masu godiya akan samun dama da yayi na jagoranchin Matasan North West na akalla wata goma sha ukku (13months), inda ya zayyana ayyuka da nasarorin da ya samu a cikin wannan lokaci da yayi yana wannan aiki.

A yayi wannan taro, ya roki Exco na Karamar Hukumar Jibia da su zabi Maigirma Hon. Salisu Yusuf Majigiri, tsohon chairman na Jam’iyyar PDP na Jahar Katsina kuma Dantakar gwamna na shekara 2023. A cewar sa, Majigiri dan  Jam’iyya ne wanda yasan kima da darajan y’ay’an Jam’iyyar PDP, kuma yana da yakini, zai yi tafiya da dukkanin y’ay’an Jam’iyya idan ya samu nasara.

“A matsayina na wanda nayi aiki da Hon. Majigiri a matsayin mai bashi shawara akan Matasa da Kungiyoyi, ina da tabbacin Majigiri zai ba mara da kunya ba, domin shi mutum ne wanda ya bauta ma Jam’iyyar PDP,  ya kuma kawo mata nasarori a Jahar Katsina, musamman wajen jagorantar kwato ma rusassun shugabanin kananan hukumomi hakkin su wajen gwamnatin APC”, cewar Hon. Hamza Jibia.

A karshe Hon. Hamza Jibia ya baiwa Exco da masu ruwa da tsaki Naira dubu dari biyu da talatin N230,000 domin biyan kudin mota, tare da Addu’ar Allah ya maida kowa gidan sa lafia.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram