Atiku Ya Ce Babu Musulmi Na Ƙwarai Da Zai Goyi Bayan Ɓatanci Ga Annabi Muhammadu –

Daga bakin daya daga cikin makusantan Alh Atiku Abubakar na katsina Alh Mas’ud Abdulqadir (DAN GURUF).

Munyi magana dashi tare da samun cikakken bayani daga bakin shi kasancewar yana cikin makusantar Alh Atiku Abubakar.

Ga abunda yace; Na yi magana da Alh Atiku Abubakar, kuma ya nisanta kanshi daga wannan magana da ake alaqanta shi da ita. Yace babu musulmi na kwarai da za’ayi batanchi ga fiyayyen halitta Annabi Muhammad Tsira da aminchi su kara tabbata a gareshi kuma ya goyi baya. Ya kara da cewa duk duniya alfarmar Annabi Muhammad (SAW) muke ci.

Don haka ina Allah wadai da wanda yayi wannan rubutu bada yawu na ba, kuma na koreshi take daga lokacin dana samu labarin faruwar lamarin.

Wannan shine bayanin da Alhaji Atiku Abubakar yayi min, inji Alh Masud DanGuruf

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram