Da Dumi-dumi: Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Kano Ya Fice Daga Jam’iyyar APC

Mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Zubairu Hamza Massu, ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki.

Bayan murabus din nasa, APC ta rasa ‘yan majalisar wakilai hudu cikin kwanaki uku.

Jam’iyyar dai ta fuskanci zazzafar sauya sheka tun bayan da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya nada Nasiru Gawuna mataimakinsa a matsayin wanda zai gaje shi.

‘Yan jam’iyyar APC daga Kano ta Kudu ba su ji dadin amincewar Gawuna da Murtala Garo daga Kano ta tsakiya da kuma Kano ta Arewa ba a zaben 2023.

Mataimakin kakakin majalisar wanda ke wakiltar karamar hukumar Sumaila daga Kano ta kudu a majalisar ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC a wata wasika da ya aikewa shugaban jam’iyyar APC na gundumar Massu.

Ko da yake bai bayyana matakin da zai dauka na gaba ba, Massu ya ce matakin ya biyo bayan tuntuba da jama’ar mazabarsa da magoya bayansa kan abubuwan da suka faru a jam’iyyarsu.

“Bayan abubuwan da suka faru a cikin jam’iyyar biyu tare da tuntubar jama’a da magoya bayana da masu ruwa da tsaki a Sumaila da Kano ta Arewa gaba daya, na rubuta domin sanar da ku kudiri na na ficewa daga jam’iyyar APC.

Wasikar ta kara da cewa, “Shawarar ta samo asali ne saboda rashin adalci, rashin isassiyar dimokuradiyya na cikin gida da kuma mayar da Kano kudu saniyar ware daga wasu damammaki.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram