Rundunar Soji Ta Cafke Jami’ai 3 Kan Saida Harsashi Ga Ƴan bindiga

An kama Sojoji 3 akan laifin saida Harsashi ga Ƴan Bindiga da ƴan ta’adda a Jahar Zamfara.

Bayanan Sirri ya bayyana cewa kama su ya biyo bayan bincike da akayi akan Harsashi 425 a Dakarun Sama na FOB a Ƙaramar Hukumar Shinkafi ta Jahar Zamfara.

An gano cewa Sojin Private Bala Nura na Dakarun FOB yana daga cikin wanda aka kama dumu-dumu yana saida Makamai da Harsashi ga Ƴan bindiga da ƴan ta’adda.

Sojan ya tabbatar da saida Harsashi kimanin kamu 100 mai nauyin 7.62 akan kuɗi Naira dubu 100.

Ya kuma tabbatar da cewa yayi alƙawarin sake saida wani Harsashin guda 1000 ga ƴan bindiga akan Naira Miliyan 1.

Nura ya kuma ambaci sunayen wasu Sojojin, Lance Corporal Shehu Mohammed da Lance Corporal Monday a matsayin masu Taimaka masa.

A halin yanzu Rundunar Soji na cigaba da bincike domin gano idan akwai wasu masu taimaka mashi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram