A ranar Asabar ne gwamnatin jihar Kaduna ta haramta duk wani nau’i na zanga-zangar addini, kamar yadda ta yi gargadin cewa za a gurfanar da duk wanda ya karya doka.
Samuel Aruwan ne ya yi wannan gargadin.
Kwamishinan Ma’aikatar Tsaro da Harkokin Cikin Gida ta Jihar Kaduna a wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar
A cewarsa, haramcin ya zama wajibi ne duba da matakin da wasu marasa kishin kasa suka dauka na shirya jerin zanga-zangar kyamar baki da suka shafi ci gaban tsaro a daya daga cikin jihohin Arewacin Najeriya.
“Gwamnatin jihar Kaduna tare da tuntubar jami’an tsaro a karkashin inuwar majalisar tsaro ta jihar Kaduna ta sanya dokar hana zanga-zangar da ta shafi harkokin addini a fadin jihar nan take,” inji shi.
A cewarsa, Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai, wanda aka sanar da shi halin da ake ciki, ya bukaci jami’an tsaro da su tabbatar da tsauraran dokar hana duk wata zanga-zangar addini a jihar.
Gwamnan ya kuma bukaci malaman addini da shugabannin al’umma da sarakunan gargajiya a fadin jihar da su kara kaimi wajen kokarin gwamnati da hukumomin tsaro na wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
“Don haka hukumomin tsaro sun yanke shawarar cewa duk wani yunkuri na mutane ko kungiyoyi na kawo cikas ga zaman lafiya a Jihar, ta hanyar zanga-zangar addini, ba za a lamunce ta ba.
“Za a dakatar da irin wannan zanga-zangar ba tare da bata lokaci ba, kuma za a gurfanar da masu kira gaban kotu,” in ji shi.
Sanarwar ta kuma bukaci ‘yan jihar da su kwantar da hankulansu yayin da suke gudanar da ayyukansu na bin doka, da kuma gaggauta kai rahoton duk wani abu da ya shafi tsaro ga ofishin jami’an tsaro na jihar Kaduna mafi kusa.