Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya sanya dokar hana fita a cikin birnin jihar sakamakon mummunar zanga-zangar da wasu matasa suka yi na neman a sako wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan Deborah Samuel bisa zargin yin batanci ga annabi Muhammad S.A.W.
Dokar hana fita za ta dauki tsawon awanni 24 tana aiki
Tunda farko kafin ayyana dokar hana fita ta sa’oi 24 gwamna Aminu Tambuwal ya gana da malaman addini a ranar Juma’a domin kwantar da tarzoma.
An dai samu tashin hankali a wasu sassan jihar Sokoto a ranar Asabar din Nan, yayin da masu zanga-zangar suka bazama kan tituna domin sakin wadanda a ka kama da ake zargi da hannu a kisan wata daliba da ake zargin sun yi batanci.
Jaridar Jakadiya ta ruwaito, yadda aka kashe Deborah Samuel, daliba mai mataki aji na 200level a Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, bisa zarginta da aikata sabo.
Masu zanga-zangar sun yi amfani da kwalaye masu rubuce-rubuce kamar, “Ku saki ‘yan uwanmu Musulmi”, Musulmi ba ‘yan ta’adda ba ne, da dai sauransu.
Gabanin zanga-zangar dai an jibge jami’an tsaro a wurare masu muhimmanci da suka hada da fadar Sarkin Musulmi.
An fara samun matsala ne bayan da marigayiyar ta yi kalaman batanci a wani group na WhatsApp da abokan karatunta suke ciki.
“Jami’an tsaron kwalejin sun shiga tsakani ne ta hanyar garzayawa da ita ofishinsu amma dalibai sun Fi karfinso, inda daga bisani suka kashe ta suka banka mata wuta,” wata majiya ta shaida wa Jaridar Daily Trust.