Najeriya Na Da Yara Miliyan 18.5 Da Ba Sa Zuwa Makaranta – UNICEF

Asusun talafawa yara na majalisar Dinkin Duniya yace yara fiye da miliyan goma sha takwas ne basa zuwa makaranta, inda fiye da Rabin adadin yara mata ne.

Wannan dai ba karamin lamari bane ga Nijeriya kasar da tafi kowace ƙasa yawan al’umma a nahiyar Afirka.

Shugabar ofishin UNICEF dake Kano Rahama Farah ne ya fadawa manema labarai cewa a kwai yara miliyan 18 da dubu dari biyar da basa zuwa makaranta, in da ya ce yara mata sun kai kashi 60 cikin dari na adadin.

Ya kara da cewa hare haren da yan ta’adda da sauran masu aikata laifukka da masu sace mutane domin neman kudin fansa ke kaiwa a makarantu yayi tasiri sosai wurin ƙaruwar lamarin.

Tun bayan da kungiyar boko haram ta sace mata yan makarantar sakandare a garin Chibok a jihar Borno da ke arewa maso gabas su fiye da 200 ake cigaba da samun irin makamancinsa a wasu makarantu da ke wasu yankunan kasar nan.

A shekarar bara yan bindiga sun sace a ƙalla yara yan makaranta fiye da dubu goma shabiyar (15000) inda aka tabbatar da mutuwar dalibai 16, kamar yadda UNICEF ya tabbatar.

Rahotan ya kara da cewa an saki wasu da aka kama bayan biyan cimma wasu yarjejeniya, yayin har yanzu ake cigaba da tsare wasu a cikin gandun daji.

UNICEF ta kara da cewa fiye da makarantu dubu goma sha day(11,000) a ka rufe saboda matsalar tsaro a Nijeriya tun watan Disambar shekara 2020, zuwa yanzu. Kuma a halin yanzu iyayen najin tsoron sanya ya yansu makarantu.

Bisa kara samun rufe makarantun da ake yi a Nijeriya , UNICEF yayi gar gadi akan yawaitar Auren wuri .

Jami’in na UNICEF ya ce a jihohin arewacin Najeriya cikin ko wadanni yara mata huɗu, ɗaya ce kawai ake iya samu wanda ta kammala karamar sakandare a yankunan karkara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram