An zabi Sheikh Mohamed bin Zayed a matsayin sabon shugaban kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.
A cewar Khaleej Times, Zayed ya gaji dan uwansa Sheikh Khalifa bin Zayed Al Nahyan, wanda ya rasu ranar Juma’a yana da shekaru 73 a duniya.
Shugaban mai shekaru 61, zai kasance shugaban kasar na uku kuma na 17 wanda ya mulki Abu Dhabi.
Majalisar koli ta tarayyar kasar ce ta sanar da zaben sa a matsayin shugan kasa ranar Asabar.
An bayyana cewa, majalisar koli ta tarayya ta gudanar da taro a fadar Al Mushrif da ke birnin Abu Dhabi inda ta zabi Sheikh Mohamed bin Zayed a matsayin shugaban kasar UAE baki daya.
Sabon shugaban zai ci gaba da mulki na tsawon shekaru biyar kafin ya samu damar sake tsayawa takara.
A ranar juma’a ne dai Sheikh Mohamed Bin Zayed ya sanar da cewa gwamnatin kasar ta ba da sanarwar kwanaki 40 na zaman makoki tare da yin umarnin ayi kasa kasa da tutoci daga ranar Juma’a.
Sannan ta dakatar da ayyukan gwamnati da masu zaman kansu na kwanaki uku na farkon zaman makoki.
Sheikh Khalifa ya zama shugaban UAE na biyu a watan Nuwamba shekarar 2004.
Ya gaji mahaifinsa a matsayin sarkin Abu Dhabi na goma 16.