Wasu ‘Yan Bundiga Sun Harbe Jigo A Jam’iyyar PDP A Jihar Akwa Ibom
An harbe wani jigo a jam’iyyar PDP a karamar hukumar OrukAnam a jihar Akwa Ibom, Sir S J Ntefre.
Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba suka harbe Ntefre a gidansa.
Maharan sun bar motar su a Ekparakwa, lokacin da suka zo domin gudanar da aika aikar tasu.
An tattaro cewa lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da misalin karfe 8:00 na safe lokacin da ‘yan bindigar suka yi yunkurin sace shi a cikin gidansa.
Wata shaidar gani da ido wacce ta bayyana kanta da Misis Sarah Williamson ta shaidawa DAILY POST cewa ‘yan bindigar sun isa gidan mamacin ne sanye da wata bakar mota kirar SUV suka fitar da shi waje yayin da sauran ‘yan kungiyar ke harbin don tsoratar da makwabta.
Ta kara da cewa harbe-harben bindigar ya janyo hankulan matasan da suka yi ta tayar da kayar baya a kan ‘yan bindigar wanda ya sa al’umma gaba daya suka fatattaki ‘yan bindigar.
Ta ce a lokacin da matasan suka fara fatattakar masu garkuwa da mutane, tuni suka yi awon gaba da jigon jam’iyyar zuwa cikin daji da ke kusa da inda suka harbe shi yayin da wasu ’yan kungiyar da ke jira a cikin mota suka yi watsi da ita suka tsere zuwa cikin daji.
“Jama’a sun fito sun yi birgima da motar daga wajen. Ban san inda suka kai shi ba amma na tabbata sun gudu sun bar motar a baya.”
An tattaro cewa matasan sun yi gaggawar bincike cikin daji inda suka gano gawar jigon jam’iyyar a kwance a cikin tafkin jininsa .
Idan dai za a iya tunawa, a ranar Lahadin da ta gabata, mako guda kacal, an yi garkuwa da limamin cocin Katolika na X Parish da ke kan hanyar Ekparakwa zuwa Etinan, kuma daga baya ya samu ‘yanci bayan kwanaki hudu a hannun masu garkuwa da mutane.
Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya ce kila kisan gillar da aka yiwa jigon jam’iyyar ba zai rasa nasaba da zaben fidda gwani na majalisar wakilai da za a yi ba.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Akwa Ibom, SP Odiko Mcdon, ya ce bai samu rahoton faruwar lamarin a hukumance ba amma ya yi alkawarin mayar da martani da zarar an sanar da hukumar.
Ba mu samu wani rahoto kan wannan ba, zan sanar da ku da zaran an min bayani,” inji shi.