Ƴan Bindiga Sun Ƙona Sakatariyar Karamar Hukuma Da Kotun Majistare A Jihar Anambra

Wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne sun kona sakatariyar karamar hukumar Idemili ta Arewa da ke Ogidi da kuma wata kotun Majistare da ke yankin.

Majiyoyi sun ce maharan sun shiga harabar ne a daren Lahadin da ta gabata don ci gaba da aikin, inda suka kona daukacin muhimman abubuwan, da kadarorin da ke cikin sakatariyar, ciki har da ginin sakatariyar.

Hotunan bidiyo da ke yawo a yanar gizo sun nuna cewa gine-ginen sun koma wayam, yayin da motocin da ke ajiye a cikin sakatariyar karamar hukumar kuma suka kone kurmus.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta kuma tabbatar da faruwar lamarin, inda ta danganta lamarin ga wadanda ba a san ko su waye ba.

DSP Toochukwu Ikenga, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar ya ce: “Eh, an tabbatar da faruwar lamarin, kuma jami’an mu sun je wurin domin dawo da zaman lafiya.

“A yanzu haka, an kashe gobarar, kuma an samu kwanciyar hankali a yankin,” Ikenga ya shaidawa wakilin DAILY POST.

Wannan dai bashine karon farko da ake samun wasu mahara suna kona sakatariyar karamar hukuma da ofisoshin ‘yan sanda a yankin kudu maso gabas ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram