Gwamnan Sokoto Tambuwal Ya Sassauta Dokar Hana Fita

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto a yau Litinin ya sassauta dokar hana fita ta sa’o’i 24 da aka kafa a babban birnin Sokoto ranar Asabar.

Yanzu dai an sassauta dokar ta zama daga magariba zuwa wayewar gari.

Gwamnan ya sanya dokar ta-ɓacin ne domin shawo kan tashe-tashen hankula da suka biyo bayan kisan da aka yi wa wata dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato da ke karatu a ajin 200 bisa zargin furta kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Ɗage dokar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai, Alhaji Isa Bajini-Galadanchi ya fitar.

Ya bayyana cewa sassauta dokar hana fitar ya biyo bayan bayanan da hukumomin tsaro suka bayar a jihar.

Ya ƙara da cewa “an sassauta dokar ne don baiwa mutane damar gudanar da kasuwancinsu na halal da sauran harkojin rayuwa,” in ji shi.

Kwamishinan ya ruwaito Gwamna Tambuwal yana shawartar mazauna yankin da su zauna lafiya tare da gargadin cewa gwamnati ba za ta lamunci karya doka ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram