Ministar Mata Ta Janye Daga Takarar Sanata A Filato

Ministar kula da Harkokin mata Pauline Fallen ta sanar da janyewa daga mukamun da taso tsayawa a baya, wato takarar Sanata a zaben 2023.

Tallen ta bayyana hakan ne s Abuja, cikin wata Sanarwa da ta fitar tare da rabata ga manema labarai a yau Litinin.

Ta kara da cewa har yanzu tana nan a matsayin ta ministar mata, domin tabbatar da walwala a gare su, tare da yaki da kalubalen da suka fuskanta.

A cewar ta daga cikin dalilan da ya sanya shugaba Buhari nada ta a wannan matsayin ya haɗar da irin gudunmawar da ake ganin zata baiwa bangaren Mata da kananan yara, a don haka ta yanke shawarar ci gaba da zama a muƙamin ministar.

Majiyar Jaridar Jakadiya dai a baya ta kawo muku rahoton yadda ministar ta bayyana kudurin ta na tsayawa takarar sanata, da nufin wakiltar Plateau ta Kudu a Majalisar dattawan Kasar nan, a ranar 8 ga watan Mayu.

Yanzu dai itace ta Uku, cikin jerin Ministocin Buhari, bayan Chris Ngige, sai kuma Abubakar Malami wadanda suma tuni suka janye daga tsayawa takarar da suka so kasance cikin masu nema.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram