NSCDC Ta Kama Mutane 2 Da Laifin Fyade Da Auren Jinsi A Jihar Nasarawa

Hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (NSCDC), reshen jihar Nasarawa, a karshen mako ta kama wasu mutane 2 da ake zargi da laifin fyade da kuma luwadi.

Da yake gabatar da mutanen biyu a hedikwatar hukumar da ke Lafia, a karshen mako, kakakin rundunar, Jerry Victor, ya bayyana cewa lamarin farko ya faru ne a ranar 20 ga watan Afrilu, 2022 a Unguwar Galadima da ke Lafiya a lokacin da wani Abubakar Abdullahi (wanda ake zargin) ya yi lalata wadda abin ya shafa mai suna Ramatu Abdullahi mai shekaru 10 ta hanyar siyan dabinonta kafin a kama shi.

Kakakin ya ci gaba da cewa, bincike ya nuna cewa ba shi ne karon farko da wanda ake zargin ya aikata irin wannan laifin ba.

Inda ya kara da cewa rahotannin likitoci sun nuna cewa wanda ake zargin yana dauke da cutar Hepatitis.

Dangane da batun luwadi, ASC Victor ya bayyana cewa: “Bayan na biyu wanda ya shafi Shaau Abdulrazag (wanda aka azabtar) mai shekaru 19 mahaifinsa, Saminu Abdulrazag ne ya kai karar wani Usman Umar mai shekaru 37 kuma lamarin ya faru a Tudun-Kauri abirnin Lafiya.

“An kama wanda ake zargin yana yunkurin aikata laifin luwadi bayan ya lallabe wanda aka azabtar akan naira 120 ko N200 ko kuma Indomie”.

Ya kara da cewa wanda ake zargin ya amsa cewa ba shi ne karon farko da ya aikata irin wannan laifin ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram