2023: Ku Guji Yin Rashin Adalci A Zaɓukan Fidda Gwani — INEC Ta Gargaɗi Jam’iyyun Siyasa

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC, a yau Talata, ta gargaɗi jam’iyyun siyasa da su guji yin rashin adalci a zaɓukan fidda-gwani domin domin ɗorewar dimokaraɗiyya a Nijeriya.

Yahaya Bello, Kwamishinan Zabe na Babban Birnin Tarayya, ne ya yi wannan kiran a wajen taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki na jam’iyyun siyasa da za a gudanar a Abuja.

A cewar Bello, kiran ya zama wajibi domin zaɓe mai inganci yana farawa ne da sahihin da kuma adalin zaɓen fidda-gwani domin tabbatar da dimokaraɗiyyar cikin gida.

Ya kara da cewa, a lokacin zaɓen kananan hukumomin brinin taraiya da aka kammala, sakamakon wasu zabukan fidda gwani da aka gudanar ya yi muni sosai da kuma kalubale a kararrakin da suka kai har kotun koli.

“Wannan ya sanya hukumar cikin kunci da damuwa da su kan su jam’iyyun siyasar ma.

“Saboda haka muna so mu tunatar da dukkan jam’iyyun siyasa cewa ya kamata su kasance masu ruwa da tsaki da kuma abokan huldar INEC kuma ya kamata su shiga cikin kishinmu na tabbatar da dorewar dimokradiyya a cikin kasa,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram