Ku Kwantar Da Hankalin Ku Kan Fashewar Tukunyar Gas – Gwamnatin Kano ga Al’umma

Gwamnatin Jihar Kano ta yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu bayan fashewar tukunyar gas a yau Talata a unguwar Sabon Gari.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Muhammed Garba ya fitar a yau Talata a Kano.

Malam Garba ya ce an shawo kan lamarin, saboda jami’an tsaro sun mamaye yankin domin ceto da kuma gudanar da bincike.

“Gwamnatin jihar za ta sanar da jama’a kan duk wani ci gaba da s ke samu,” inji shi.

Malam Garba ya gargadi mazauna garin kan labaran ƙarya da kuma jita-jita kan lamarin.

Ya kuma yi zargin cewa fashewar ta faru ne a kusa da wata makaranta, inda ya ce ya faru ne a kusa da wani kantin sayar da abincin, daura da makarantar da ke kan titin Aba, Sabon Gari, Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram