Ƴan bindiga a ranar Talata da daddare, sun kai gidan Shugaban Ƙaramar Hukumar Iko ta Jahar Ebonyi Steve Orogwu, tare da kashe makusantan shi.
Jaridar PUNCH ta gano cewa ƴan bindigar su. Kashe Jami’in tsaro dake kan aiki, tare da ƙona gida Orogwu.
Amma an gano cewa Shugaban Ƙaramar Hukumar baya cikin gidan a lokacin da ƴan bindigar aka yi ƙawanya, gami da ƙaddamar da harin.
Majiya mai ƙarfi tace ƴan bindigar sun zo gidan Shugaban Ƙaramar Hukumar dake Ekpaomaka, a daren ranar Talata.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Mr. Orogwu ya Tabbatar da faruwar lamarin ga Manema Labaru a safiyar ranar Laraba.
A cewar sa “sun kai ma gidana hari dake Ikwo da daddare, tare da kashe Babban Yaya na, ƴaƴan sa biyu da Jami’in tsaro.
Sun kuma ƙona gidan dake wurin, inda a halin yanz an kai gawar zuwa Ɗakin Ajiye gawa na Abakaliki.
Yankin Kudu maso Gabas a ranar Talata ya fuskanci dokar zaman gida da Ƙungiyar Ƴan ta’addan IPOB suka umarta.
A saboda haka, har yanzu ba’a tabbatar da abinda ya haddasa kai harin ba, ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton a ranar Laraba da safe.
Mai Magana da Yawun Rundunar Ƴan Sandan Jahar Mrs Loveth Odah tace tana wani aiki da aka umarce ta, ta gudanar a lokacin da aka nemi jin tabakin ta.
Har yanzu bata maido amsa akan saƙon da aka tura mata ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.