APC Ta Sake Ɗaga Ranakun Zaɓen Fitar Da Gwani

Jam’iyya mai mulki a Najeriya ta ce za a gudanar da zaɓukann fitar da gwani na gwamnoni da ƴan majalisar wakilai a ranar 26 ga watan Mayu.

Kakaki Network ta ruwaito BBC na cewa batun ya zo ne a wani sabon jadawalin da jam’iyyar ta fitar a yau Laraba a shafinta na Twitter, ya nuna cewa zaɓen fitar da gwani na majalisar dattawa shi kuma ya koma ranar 27 ga watan Mayu haka ma na ƴan majalisar dokoki ta jihohi.

Sannan kuma za’a gudanar da zaɓen fitar da gwani na shugaban ƙasa a ranakun 29 da 30 ga watan Mayu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram