Kotu Taƙi Bada Belin Nnamdi Kanu

Babbar Kotun Tarayya dake zaman ta a Abuja a ranar Laraba ta hana bada belin Shugaban Ƙungiyar Tsagerun Kafa Ƙasar Biafra Nnamdi Kanu.

Mai Shari’a Binta Nyako a shari’ar data gudanar, tace tunda aka bada Kanu beli a Shekarar 2017 ya gudu, dole Kotu ta gano dalilin daya sanya ya tsere daga belin da aka bashi kafin a bada shi wani.

Daga nan Mai Shari’a Nyako sai ta kori buƙatar bada shi beli kamar yadda Kamfanin Dillancin Labaru na Ƙasa ya ruwaito.

Kotu a ranar 8 daga watan Afrilu ta cire Gwamnatin Tarayya daga zargin cewa Shugaban IPOB an matsa mashi ne domin ya gudu zuwa kasar waje.

Nyako a hukuncin data gabatar tace tunda ana zargin shi akan ta’addanci to za’a iya kama shi a ko’ina aka gashi.

Mai Shari’ar wadda ta kori buƙatar Kanu na cire wata ƙarar da aka ƙara shigar, ta amince da guda bakwai da aka shigar akan Shugaban IPOB.

Nyako tace Gwamnatin Tarayya ta hanyar ofishin Antoni-Janar na Ƙasa zata iya shigar da sabbin ƙararraki daga 1, biyu, 3, 4, 5, 8, zuwa 15.

Haka zalika bayan ta duba sabbin ƙararraki da aka shigar tace suna kama ce ceniya, amma bata bayyana wani umarni da zata ɗauka ba.

Nyako ta ƙara dacewa umarnin da aka bayar kan bayyana IPOB a matsayin Ƴan ta’adda tace har yanzu tana nan, sai dai in Kotun Ɗaukaka Ƙara ta cire ta.

Ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, har yanzu ana cigaba da sauraren ƙarar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram