Nan Da Kwanaki 3 Masu Zuwa Jihohin Legas, Abuja, Kano,Za Su Fuskanci Ruwan Sama Mai Karfi – NiMet

Nan Da Kwanaki 3 Masu Zuwa Jihohin Legas, Abuja, Kano,Za Su Fuskanci Ruwan Sama Mai Karfi – NiMet

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya, NiMet, ta shaidawa mazauna babban birnin tarayya Abuja da jihohin Bauchi, Gombe, Plateau, Taraba, Benue, Cross River, Kwara, Neja, da Kogi da su tashi tsaye domin tsammanin samu ruwan sama mai matsakaicin karfi cikin kwanaki uku masu zuwa.

Hukumar ta kuma yi hasashen yanayi makamancin haka a jihohin Legas, Oyo, Ogun, Ondo, Osun, Ekiti, Kogi, FCT, Nassarawa, Edo, Delta, Akwa Ibom, Ribas, Borno, Yobe, Jigawa, Kano, Imo, Abia da kuma jihar Ebonyi. daga safiyar Laraba zuwa yammacin Juma’a,

Yawancin sassan arewa maso yammacin kasar ana sa ran samun ruwan sama kadan, in ji Nimet a cikin shawarwarin yanayin da ta ke yi a jiya Talata.

“Sakamakon ruwan sama matsakaici da ake sa ran za a samu nan da kwanaki uku masu zuwa, akwai yuwuwar afkuwar ambaliyar ruwa da matsugunai,” in ji hukumar.

Ya kara da cewa “akwai iya samun cikas na cunkoson ababen hawa saboda ambaliya ko rufe tituna, da rage ganuwa, da yuwuwar lalata gidajen kasa da kuma yiwuwar dakile ayyukan jirgin.”

Ana sa ran ruwan saman zai kasance tare da iska mai ƙarfi, walƙiya da tsawa, don haka akwai yuwuwar faɗuwar gine-gine masu rauni da ƙauracewa gine-ginen na wucin gadi, in ji NiMet.

Don haka, ta shawarci jama’a da su kasance masu kamun kai, da cire na’urorin lantarki kafin lokacin, ba lokacin guguwar ba, kuma a guji tsayawa ko ajiye motoci a karkashin bishiyu gwargwadon iko.

NiMet ta bukaci hukumomin gaggawa da su kasance cikin shiri kuma su ci gaba da sa ido don guje wa guraben da ba su da tushe da kuma kwararar ruwa mai saurin gudu.

Haka kuma ta shawarci jama’a da su kasance cikin shiri don wadannan abubuwan domin kaucewa barna daga hadurran da suka shafi ruwan sama.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Social media & sharing icons powered by UltimatelySocial
YouTube
YouTube
Instagram